9 Yuli 2020 - 12:48
Guterres Ya Yi Tir Da Kasashen Da Ke Sanya Hannu A Rikicin Libiya

Babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guteres, ya yi, Allah-wadai da kakkausar murya game da kasashen ketare da ke sanya hannu a rikicin kasar Libiya.

(ABNA24.com)  Ya ce MDD, za ta ci gaba da aiki tare da bangarorin da ke rikici da juna don cimma yarjejeniyar tsagaita wuta da kuma komawa hanyar siyasa

A cewarsa Libiya dai yanzu na fama da katsalandan na kasashen ketare ya hada da kai miyagun makamai da shigar da mayaka a kasar, wanda kuma hakan ya saba wa takunkumin makaman da Majalisar Dinkin Duniya ta sanya wa kasar ta Libiya.

Shi ma shugaban Kwamitin Sulhu kuma Ministan Harkokin Wajen Jamus, Heiko Maas ya cacaki kasashen da ke katsalanda cikin rikicin na Libiya, ta hanyar shigar da kayan soji, da mayaka da kuma makamai.

Shi kuwa Ministan harkokin Jamhuriyar Nijar, Kalla Hankurau cewa ya yi Libiya ba ta bukatar makamai ko sojin haya, illah kawai a lalubo hanyoyin sulhu tsakanin bangarorin dake rikici a kasar.

342/